31 Maris 2022 - 17:18
Qais Saeed Ya Rusa Majalisar Dokokin Kasar Tunisia

A yammacin Larabar nan ne shugaban kasar Tunisiya Qais Saied ya sanar da rusa majalisar dokokin kasar, bayan dakatar da aikinta tun ranar 25 ga watan Yulin 2021.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - A cikin wani jawabi da Qais Saeed ya yi, ya ce, "Bisa doka ta 72 a kundin tsarin mulkin kasar, a yau, a wannan lokaci mai dimbin tarihi, na sanar da rusa majalisar dokokin kasar, domin kiyaye kasa da cibiyoyi, da kuma kiyaye al'ummar kasar Tunisia."

Shugaban ya yi la’akari da cewa taron wasu ‘yan majalisar wakilai da aka dakatar da aikinsu daga nesa, wani yunkuri ne na juyin mulki da bai yi nasara ba, inda ya bayyana cewa sun shirya makarkashiyar ta’addanci a cikin gida da waje.

Ya jaddada cewa za a tuhume su da laifi, kuma Ministan Shari’a ya dauki matakin shigar wata kara a gaban masu gabatar da kara.

Shugaban ya yi gargadin cewa duk wata hanya ta tashin hankali za ta fuskanci doka, domin a cewarsa jihar ba za ta taba zama abin wasa a hannun wadanda suka yi yunkurin kifar da ita ba.

Da yake jawabi ga 'yan Tunisiya, Saeed ya ce, "Mu duka mu zauna lafiya, domin cibiyoyin gwamnati ne akwai za su kare kasar daga masu tsattsauran ra'ayi da manufarsu ta rusa kasa" a cewarsa.

Dangane da taron majalisar dokokin kasar da aka dage, wanda ya gamu da cikas, shugaban kasar Tunisiya ya bayyana a ganawarsa da firaministan kasar Najla Boden cewa, fitina ta fi kisa tsanani, inda ya kara da cewa, "Idan har ana son a raba kasar da haifar da fitina, to, a kakkae hannu masu son tayar da ita.

Qais Saeed ya jaddada cewa "abin da suke yi wata makarkashiya ce a fili ga tsaron jihar."

Ya kara da cewa, "An ba mu amanar tsaron kasar Tunisia, hadin kai da ci gaba, kuma ba za mu bari masu cin zarafi su ci gaba da kai hare-hare kan cibiyoyin gwamnati ba."

Ya kara da cewa, "Ba za mu bar su su ci gaba da ayyukansu da ke bayyana a kasashen waje ba."

342/